Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 3:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya bar waɗansu al'ummai a ƙasar domin ya jarraba Isra'ilawan da ba su san yaƙin Kan'ana ba.

2. Ya yi haka ne domin ya koya wa tsararrakin Isra'ila yaƙi, wato waɗanda ba su taɓa yin yaƙi a dā ba.

3. Al'umman da suka ragu a ƙasar su ne, birane biyar na Filistiyawa, da dukan Kan'aniyawa, da Sidoniyawa, da Hiwiyawa da suke zaune a Dutsen Lebanon, tun daga Dutsen Ba'alharmon har zuwa mashigin Hamat,

4. don a jarraba Isra'ilawa da su, a gani ko za su yi biyayya da umarnan Ubangiji da ya ba kakanninsu ta hannun Musa.

5. Saboda haka jama'ar Isra'ila suka zauna tare da Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.

6. Suka yi aurayya da su, suka kuma yi sujada ga gumakansu.

7. Jama'ar Isra'ila kuwa suka manta da Ubangiji Allahnsu, suka yi masa zunubi, suka yi wa gumakan nan Ba'al da Ashtarot sujada.

8. Domin haka Ubangiji ya husata ƙwarai da Isra'ilawa, sai ya bashe su ga Kushan-rishatayim, Sarkin Mesofotamiya. Jama'ar Isra'ila kuwa suka bauta masa shekara takwas.

9. Amma sa'ad da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, sai Ubangiji ya ta da Otniyel, ɗan Kenaz, ƙanen Kalibu don ya ceci Isra'ilawa.

10. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko masa domin ya hukunta Isra'ilawa. Ya fita ya yi yaƙi da Kushan-rishatayim, Sarkin Mesofotamiya. Ubangiji kuwa ya ba da sarkin a hannun Otniyel, ya rinjaye shi.

11. Ƙasar ta sami zaman lafiya shekara arba'in sa'an nan Otniyel, ɗan Kenaz ya rasu.

12. Jama'ar Isra'ila kuma suka sāke yin zunubi a gaban Ubangiji, Ubangiji kuwa ya sa Eglon Sarkin Mowab ya yi ƙarfi, domin ya yi gaba da su.

Karanta cikakken babi L. Mah 3