Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 21:15-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Sai mutanen suka yi juyayin mutanen Biliyaminu domin Ubangiji ya naƙasa kabila daga kabilar Isra'ila.

16. Saboda haka dattawan taron jama'a suka ce, “Ƙaƙa za mu yi da waɗanda suka ragu da ba su sami mata ba, da yake an hallaka matan kabilar Biliyaminu?”

17. Sai suka ce, “Tilas, waɗanda suka ragu daga mutanen Biliyaminu su sami gādo domin kada a shafe kabila daga cikin Isra'ila,

18. amma fa ba za mu iya aurar musu da 'ya'yanmu mata ba.” Sun faɗi haka ne kuwa, domin sun riga sun rantse cewa, “Duk wanda ya aurar da 'yarsa ga mutumin Biliyaminu la'ananne ne.”

19. Suka kuma ce, “Ga shi, idin Ubangiji na shekara shekara a Shilo ya kusa.” (Shilo tana arewacin Betel, kudu da Lebona, gabas da hanyar da take tsakanin Betel da Shekem.)

20. Suka umarci mutanen Biliyaminu suka ce, “Ku tafi ku yi kwanto a gonakin inabi,

21. ku lura, idan 'yan matan Shilo sun fito domin su yi rawa, sai ku fito daga cikin gonakin inabi, kowa ya kama daga cikin 'yan matan da ƙarfi, ya sami mata ke nan, ya tafi da ita a ƙasar Biliyaminu.

22. Sa'ad da iyayensu ko 'yan'uwansu sun kawo ƙara gare mu, za mu ce musu, ‘Ku bar mana su, muna roƙonku, domin ba daga wurin yaƙi muka kamo su domin su zama matanmu ba. Amma tun da ba ku ba mu su ba, ba ku da laifin ta da alkawari.’ ”

23. Haka kuwa mutanen Biliyaminu suka yi. Suka kama budurwai gwargwadon yawansu daga cikin masu rawa. Sa'an nan suka koma zuwa yaƙin ƙasarsu ta gādo. Suka sāke gina garuruwansu, suka zauna.

24. Haka nan kuma sauran mutanen Isra'ila suka tashi daga can. Kowa ya tafi wurin kabilarsa, da iyalinsa, da abin da ya mallaka.

25. A lokacin ba sarki a Isra'ila, sai kowa ya yi ta yin abin da ya ga dama.

Karanta cikakken babi L. Mah 21