Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 20:5-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sai mutanen Gibeya suka kewaye gidan da nake da dare, suna neman kashe ni, da ba su same ni ba, sai suka yi wa ƙwarƙwarata faɗe har ya kai ta ga mutuwa.

6. Ni kuwa na ɗauki gawarta na yanyanka gunduwa gunduwa na aika cikin ƙasar gādon Isra'ila duka, gama waɗannan mutane sun aikata abin ƙyama da abin kunya ga dukan Isra'ila.

7. Dukanku nan Isra'ilawa ne, me za mu yi a kan wannan al'amari?”

8. Dukan jama'a kuwa suka tashi gaba ɗaya, suna cewa, “Daga cikinmu ba wanda zai koma alfarwarsa ko kuwa gidansa.

9. Wannan shi ne abin da za mu yi wa Gibeya, mu zaɓi waɗansunmu su fāɗa mata da yaƙi.

10. Kashi ɗaya daga goma na Isra'ilawa su ba da abinci ga sojoji. Sauran jama'a kuwa su je su hukunta Gibeya saboda muguntar da ta aikata cikin Isra'ila.”

11. Saboda haka dukan mutanen Isra'ila suka taru niyya ɗaya domin su fāɗa wa garin da yaƙi.

12. Kabilar Isra'ila kuwa suka aiki manzanni ga kabilar Biliyaminu suka ce, “Wace irin mugunta ce wannan da kuka aikata?

Karanta cikakken babi L. Mah 20