Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 2:18-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Sa'ad da Ubangiji ya naɗa musu mahukunci, yakan taimake shi, ya kuwa cece su daga abokan gāba dukan kwanakin mahukuncin. Gama Ubangiji ya ji ƙansu saboda nishinsu, da zaluncin da ake yi musu.

19. Amma idan mahukuncin ya rasu, sai su sāke kaucewa, su yi zunubi fiye da na kakanninsu. Suna bin gumaka, suna bauta musu, suna kuma yi musu sujada, ba su daina mugayen ayyukansu na rashin aminci da taurin zuciya ba.

20. Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa ya ce, “Saboda al'umman nan ta ta da alkawarina wanda na yi da kakanninsu, ba su yi biyayya da maganata ba,

21. don haka daga nan gaba ba zan ƙara kore musu wata al'umma daga cikin al'umman da Joshuwa ya rage kafin rasuwarsa ba.

22. Da haka ne zan jarraba Isra'ilawa, in gani ko za su mai da hankali su yi tafiya cikin hanyata, kamar yadda kakanninsu suka yi, ko kuwa ba za su yi ba.”

23. Don haka Ubangiji ya bar waɗannan al'ummai, bai kore su nan da nan ba, bai kuma ba da su ga Joshuwa ba.

Karanta cikakken babi L. Mah 2