Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 19:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A lokacin nan ba sarki a Isra'ila. Sai wani Balawen da yake zama a wani lungu na ƙasar tudu ta Ifraimu ya ɗauko wata mace daga Baitalami ta Yahudiya ta zama ƙwarƙwararsa.

2. Ƙwarƙwarar kuwa ta ji haushinsa, ta koma gidan mahaifinta a Baitalami ta Yahudiya. Ta zauna a can har wata huɗu.

3. Sa'an nan mutumin ya tafi ya yi bikonta. Ya tafi da baransa da jaki biyu. Da ya zo gidan mahaifinta, sai ta shigo da shi gidan, mahaifin ya karɓe shi da farin ciki.

4. Mahaifin macen ya i masa ya dakata, sai ya tsaya har kwana uku. Suka ci suka sha tare.

5. A safiyar rana ta huɗun, suka tashi tun da wuri, domin su yi shirin tafiya, amma mahaifin matar ya ce masa, “Ka dakata ka ƙara cin abinci tukuna sa'an nan ka tafi.”

6. Su biyu kuwa suka zauna suka ci suka sha tare. Har yanzu mahaifin mace ya sāke ce masa, “Ina roƙonka ka ƙara kwana, ka saki jikinka ka more.”

7. Sa'ad da mutumin ya tashi zai tafi sai mahaifin macen ya roƙe shi, ya kuma kwana.

8. A rana ta biyar, sai mutumin ya tashi da wuri don ya tafi amma mahaifin macen ya ce masa, “Ka zauna ka ci abinci tukuna har rana ta yi sanyi.” Dukansu biyu suka zauna suka ci tare.

9. Sa'ad da mutumin, da ƙwarƙwararsa, da baransa sun tashi za su tafi, sai mahaifin macen kuma ya ce masa, “Ga shi, rana ta kusan faɗuwa, yamma kuwa ta yi, ina roƙonka, ka sāke kwana ka ji wa ranka da:di, sa'an nan ka yi sammako gobe ka kama hanyarka zuwa gida.”

Karanta cikakken babi L. Mah 19