Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 16:5-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Shugabannin Filistiyawa, su biyar suka je wurinta suka ce mata, “Ki yi masa kirsa, don ki san dalilin irin ƙarfin nan nasa, da kuma yadda za mu yi maganinsa, mu ɗaure shi don mu rinjaye shi. Kowannenmu zai ba ki shekel dubu da ɗari (1,100).”

6. Delila kuwa ta ce wa Samson, “Ina roƙonka ka faɗa mini inda babban ƙarfin nan naka yake, da kuma yadda za a ɗaure ka ka rasa kuzari.”

7. Samson ya ce mata, “Idan an ɗaure ni da sababbin tsarkiyoyi guda bakwai, waɗanda ba su bushe ba, to, sai in rasa ƙarfi, in zama kamar kowa.”

8. Sai shugabannin Filistiyawa suka kawo wa Delila sababbin tsarkiyoyi guda bakwai waɗanda ba su bushe ba. Ta kuwa ɗaure shi da su.

9. Tana kuwa da mutane a laɓe cikin wani ɗaki, sai ta ce masa, “Ga Filistiyawa a kanka, Samson!” Da jin haka, sai ya katse tsarkiyoyi kamar zare idan an sa masa wuta. Asirin ƙarfinsa kuwa bai sanu ba.

10. Delila kuma ta ce wa Samson, “Ga shi, ka yi mini ba'a, ka ruɗe ni. Ina roƙonka, ka faɗa mini yadda za a ɗaure ka.”

11. Ya ce mata, “Idan suka ɗaure ni da sababbin igiyoyi waɗanda ba a yi amfani da su ba, to, zan rasa ƙarfi, in zama kamar kowa.”

12. Sai Delila ta ɗauki sababbin igiyoyi, ta ɗaure shi da su, sa'an nan ta ce masa, “Ga Filistiyawa na zuwa kanka, Samson!” Amma ya katse igiyoyin da ta ɗaure shi da su kamar silin zare. Mutanen kuwa na nan laɓe a wani ɗaki.

13. Delila ta ce wa Samson, “Har yanzu dai, ka maishe ni shashasha, kana ta ruɗina. Ka faɗa mini yadda za a ɗaure ka.”Ya ce mata, “Idan kin saƙa tukkwayen bakwai waɗanda suke kaina haɗe da zare, kika buga da akwasha sai in rasa ƙarfi, in zama kamar kowa.”

14. Sa'ad da yake barci, Delila ta saƙa tukkwayen nan bakwai da suke kansa haɗe da zare, ta buga da akwasha, sa'an nan ta ce masa, “Ga Filistiyawa a kanka, Samson!” Da ya farka daga barcin, sai ya tumɓuke akwashar, da zaren.

Karanta cikakken babi L. Mah 16