Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 16:14-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Sa'ad da yake barci, Delila ta saƙa tukkwayen nan bakwai da suke kansa haɗe da zare, ta buga da akwasha, sa'an nan ta ce masa, “Ga Filistiyawa a kanka, Samson!” Da ya farka daga barcin, sai ya tumɓuke akwashar, da zaren.

15. Delila ta ce masa, “Ƙaƙa za ka ce kana ƙaunata, alhali kuwa ba na a zuciyarka? Sau uku ke nan ka maishe ni shashasha, ba ka faɗa mini inda ƙarfin nan naka yake ba.”

16. Sa'ad da ta fitine shi yau da gobe da yawan maganganunta, ta tunzura shi, sai ransa ya ɓaci kamar zai mutu.

17. A ƙarshe ya faɗa mata ainihin gaskiyar, ya ce mata, “Ba a taɓa aske gashin kaina ba, gama ni keɓaɓɓe ga Ubangiji ne tun daga cikin uwata. Idan aka yi mini aski, to, ƙarfina zai rabu da ni, in zama marar ƙarfi kamar kowa.”

18. Sa'ad da Delila ta gane ya faɗa mata ainihin gaskiya, sai ta aika a kirawo shugabannin Filistiyawa tana cewa, “A wannan karo ku zo, domin ya faɗa mini ainihin gaskiyar.” Shugabannin Filistiyawa kuwa suka zo wurinta da kuɗi a hannu.

19. Ta kuwa sa shi ya yi barci a cinyoyinta, sai ta kira wani mutum, ta sa shi ya aske tukkwayen nan bakwai waɗanda suke kansa. Sa'an nan ta yi ƙoƙari ta sa ya harzuƙa, amma ƙarfinsa ya rabu da shi.

20. Ta ce masa, “Ga Filistiyawa a kanka, Samson!”Sai ya farka daga barcinsa, ya ce, “Zan fita kamar yadda na saba yi koyaushe, in miƙe jikina.” Ashe, bai sani ba, Ubangiji ya rabu da shi.

21. Filistiyawa fa suka kama shi, suka ƙwaƙule idanunsa, suka gangara da shi zuwa Gaza. Suka ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla. Ya yi ta niƙa a kurkuku.

22. Amma gashin kansa ya fara tohowa.

23. Shugabannin Filistiyawa kuwa suka taru domin su miƙa babbar hadaya ga allahnsu, Dagon. Suka raira waƙa, suka ce, “Allahnmu ya ba da Samson, maƙiyinmu a hannunmu!”

Karanta cikakken babi L. Mah 16