Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 16:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga can Samson ya tafi Gaza, inda ya ga wata karuwa, sai ya shiga wurinta.

2. Aka faɗa wa mutanen Gaza, Samson yana nan. Suka kewaye wurin, suka yi fakonsa a ƙofar garin dukan dare. Suka yi shiru dukan dare, suka ce wa junansu, “Za mu jira sai gari ya waye sa'an nan mu kashe shi.”

3. Amma Samson ya yi kwanciyarsa har tsakar dare. Sa'an nan ya tashi ya kama ƙyauren ƙofar birnin, da madogarai biyu na ƙofar, ya tumɓuke su. Ya saɓe su a kafaɗarsa, ya kai su kan dutsen da yake a gaban Hebron.

4. Bayan wannan kuma sai ya kama ƙaunar wata mace mai suna Delila a kwarin Sorek.

5. Shugabannin Filistiyawa, su biyar suka je wurinta suka ce mata, “Ki yi masa kirsa, don ki san dalilin irin ƙarfin nan nasa, da kuma yadda za mu yi maganinsa, mu ɗaure shi don mu rinjaye shi. Kowannenmu zai ba ki shekel dubu da ɗari (1,100).”

6. Delila kuwa ta ce wa Samson, “Ina roƙonka ka faɗa mini inda babban ƙarfin nan naka yake, da kuma yadda za a ɗaure ka ka rasa kuzari.”

7. Samson ya ce mata, “Idan an ɗaure ni da sababbin tsarkiyoyi guda bakwai, waɗanda ba su bushe ba, to, sai in rasa ƙarfi, in zama kamar kowa.”

8. Sai shugabannin Filistiyawa suka kawo wa Delila sababbin tsarkiyoyi guda bakwai waɗanda ba su bushe ba. Ta kuwa ɗaure shi da su.

Karanta cikakken babi L. Mah 16