Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 13:18-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Mala'ikan Ubangiji ya ce masa, “Don me kake tambayar sunana? Sunana asiri ne.”

19. Manowa kuwa ya yanka ɗan akuya, ya kuma kawo hadayar gāri, ya miƙa a kan dutse ga Ubangiji, mala'ika kuma ya yi al'ajabi. Manowa da matarsa suka yi kallo.

20. Sa'ad da harshen wutar ya hau zuwa samaniya daga bagaden, sai mala'ikan Ubangiji ya hau zuwa sama ta cikin harshen wutar bagaden. Manowa da matarsa sun gani, suka fāɗi a fuskokinsu a ƙasa.

21. Mala'ikan Ubangiji bai sāke bayyana ga Manowa da matarsa ba. Manowa kuma ya gane mala'ikan Ubangiji ne.

22. Manowa ya ce wa matarsa, “Ba shakka za mu mutu gama mun ga Ubangiji!”

23. Amma matarsa ta ce masa, “Da Ubangiji yana so ya kashe mu, ai, da bai karɓi hadayar ƙonawa da hadayar gārinmu ba, da kuma bai nuna mana, ko ya faɗa mana waɗannan abubuwa ba.”

24. Matar kuwa ta haifi ɗa, aka raɗa masa suna Samson. Yaron ya yi girma, Ubangiji ya sa masa albarka.

25. Ruhun Ubangiji ya fara iza shi, sa'ad da yake a zangon Dan, tsakanin Zora da Eshtawol.

Karanta cikakken babi L. Mah 13