Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 13:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Isra'ilawa kuma suka sāke yi wa Ubangiji zunubi, sai Ubangiji ya ba da su a hannun Filistiyawa shekara arba'in.

2. Akwai wani mutumin Zora daga kabilar Dan, sunansa Manowa, matarsa bakarariya ce, ba ta haihuwa.

3. Ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare ta, ya ce mata, “Ga shi, ke bakarariya ce, ba ki haihuwa, amma yanzu za ki yi ciki, za ki kuwa haifi ɗa.

Karanta cikakken babi L. Mah 13