Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 11:28-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Amma Sarkin Ammonawa bai kula da saƙon da Yefta ya aika masa ba.

29. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko wa Yefta, sai ya tashi ratsa Gileyad da Manassa zuwa Mizfa ta Gileyad, daga can ya haura zuwa wurin Ammonawa.

30. Yefta kuwa ya yi wa'adi ga Ubangiji, ya ce, “Idan dai ka ba da Ammonawa a hannuna,

31. duk abin da ya fara fitowa daga ƙofar gidana don ya tarye ni, sa'ad da na komo daga yaƙin Ammonawa da nasara, zai zama na Ubangiji, zan kuwa miƙa shi hadaya ta ƙonawa.”

32. Yefta ya haye zuwa wurin Ammonawa domin ya yi yaƙi da su. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannunsa.

33. Ya karkashe su da mummunan kisa tun daga Arower zuwa yankin Minnit, har zuwa Abel-keramim. Ya cinye biranensu guda ashirin. Da haka Ammonawa suka sha kāshi a hannun Isra'ilawa.

34. Da Yefta ya koma gidansa a Mizfa, sai ga 'yarsa, tilo ta fito da kiɗa da rawa don ta tarye shi. Ita ce kaɗai 'yarsa, banda ita ba shi da ɗa ko 'ya.

35. Sa'ad da ya gan ta sai ya yayyage tufafinsa, ya ce, “Kaito, 'yata, kin karya mini gwiwa, kin zamar mini babban dalilin wahala. Na riga na yi wa'adi ga Ubangiji, ba kuwa zan iya warware shi ba.”

36. Sai ta ce masa, “Baba, idan ka riga ka yi wa'adi ga Ubangiji, sai ka yi da ni bisa ga wa'adinka, da yake Ubangiji ya ɗau maka fansa a kan Ammonawa, abokan gābanka.”

Karanta cikakken babi L. Mah 11