Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 6:17-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Ya kuma miƙa rago don hadaya ta salama ga Ubangiji tare da kwandon abinci, da ƙosai. Firist ɗin kuma zai miƙa hadaya ta gari, da hadaya ta sha.

18. Sai kuma keɓaɓɓen ya aske sumarsa a ƙofar alfarwa ta sujada, sa'an nan ya kwashe sumar, ya zuba cikin wutar da take ƙarƙashin hadaya ta salama.

19. Firist ɗin zai ɗauki dafaffiyar kafaɗar ragon, da malmala guda marar yisti daga cikin kwando, da ƙosai guda, ya sa su a tafin hannun keɓaɓɓen bayan da keɓaɓɓen ya riga ya aske sumarsa.

20. Firist ɗin zai haɗa su don yin hadayar kaɗawa a gaban Ubangiji. Za su zama rabo mai tsarki na firist tare da ƙirjin da aka kaɗa da cinyar da aka yi hadayar ɗagawa da ita. Bayan haka keɓaɓɓen ya iya shan ruwan inabi.

21. Wannan ita ce ka'ida a kan keɓaɓɓe wanda ya ɗau wa'adi. Hadayarsa ga Ubangiji za ta zama bisa ga keɓewarsa, banda kuma abin da ya iya bayarwa. Sai ya cika wa'adin da ya ɗauka bisa ga ka'idar keɓewarsa.

22. Ubangiji ya umarci Musa

23. ya faɗa wa Haruna da 'ya'yansa maza, su sa wa Isra'ilawa albarka haka, su ce musu,

24. “Ubangiji ya sa muku albarka, ya kiyaye ku.

25. “Ubangiji ya sa fuskarsa ta haskaka ku, ya yi muku alheri.

26. “Ubangiji ya dube ku da idon rahama, ya ba ku salama.”

Karanta cikakken babi L. Kid 6