Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 5:16-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Sai firist ya kawo ta kusa, ya tsai da ita a gaban Ubangiji.

17. Ya ɗebo ruwa mai tsarki a cikin kasko, ya kuma ɗauki ƙurar ƙasar da take a alfarwa ta alkawari ya zuba a ruwan.

18. Sa'an nan firist zai kwance gashin kanta, ya sa hadaya ta gari don tunawa a hannuwanta, hadayar gari ce ta kishi. Ya riƙe ruwan nan mai ɗaci da yake kawo la'ana a hannunsa.

19. Sa'an nan zai sa ta ta yi rantsuwa, ya ce mata, “Idan wani mutum bai kwana da ke ba, to, bari ki kuɓuta daga la'anar da ruwan nan mai ɗaci zai kawo.

20. Amma idan kin kwana da wani mutum wanda ba mijinki ba ne,

21. bari Ubangiji ya sa sunanki ya la'antu cikin jama'arki, ya sa cinyarki ta shanye, cikinki kuma ya kumbure.

22. Bari ruwan nan ya shiga cikinki, ya sa cikinki ya kumbure, cinyarki kuma ta shanye.”Sai matar ta amsa, ta ce, “Amin, amin, Ubangiji ya sa ya zama haka.”

23. Firist ɗin zai rubuta waɗannan la'anoni a cikin littafi sa'an nan ya wanke rubutun da ruwan nan mai ɗaci.

24. Ya sa matar ta shanye ruwa wanda yake kawo la'ana, sai ruwan ya shiga cikinta, ya zama la'ana mai ɗaci.

25. Firist kuma zai karɓi hadaya ta gari don kishi a hannun matar, ya kaɗa ta a gaban Ubangiji. Sa'an nan ya kai wurin bagade.

26. Sai ya ɗibi garin hadaya cike da tafin hannu don yin hadayar tunawa, ya ƙone shi a bisa bagaden, bayan wannan ya sa matar ta sha ruwan.

27. Bayan da ya sa ta ta sha ruwan, idan ta ƙazantar da kanta, ta kuwa ci amanar mijinta, ruwan nan mai kawo la'ana zai shiga cikinta ya zama la'ana mai ɗaci, cikinta zai kumbure, cinyarta ta shanye, matar kuwa za ta zama la'ananniya cikin jama'arta.

28. Amma idan matar ba ta ƙazantar da kanta ba, ita tsattsarka ce, za ta kuɓuta, har ta haifi 'ya'ya.

Karanta cikakken babi L. Kid 5