Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 33:47-56 Littafi Mai Tsarki (HAU)

47. Da suka tashi daga Almon-diblatayim, suka sauka a duwatsun Abarim a gaban Nebo.

48. Daga duwatsun Abarim suka sauka a filayen Mowab kusa da Urdun daura da Yariko.

49. Suka sauka kusa da Urdun, suka kakkafa alfarwansu tun daga Betyeshimot har zuwa Abel-shittim, a filayen Mowab.

50. Sai Ubangiji ya yi magana da Musa a filayen Mowab kusa da Urdun, daura da Yariko, ya ce

51. ya faɗa wa jama'ar Isra'ila, “Sa'ad da kuka haye Urdun zuwa ƙasar Kan'ana,

52. sai ku kori dukan mazaunan ƙasar daga gabanku ku rurrushe sassaƙaƙƙun duwatsunsu, da siffofinsu na zubi, da masujadansu.

53. Sa'an nan ku mallaki ƙasar, ku zauna a ciki,gama na ba ku ƙasar, ku mallake ta.

54. Za ku rarraba wa kanku gādon ƙasar kabila kabila ta hanyar jefar kuri'a. Za ku ba babbar kabila babban rabo, ƙaramar kabila kuwa ku ba ta ƙaramin rabo. Inda duk kuri'a ta fāɗa wa mutum, nan ne zai zama wurinsa. Bisa ga kabilan kakanninku za ku gāji ƙasar.

55. Amma idan ba ku kori mazaunan ƙasar daga gabanku ba, to, waɗannan da kuka bari cikinta za su zama haki a idanunku, da ƙayayuwa a kwiyaɓunku. Za su yi ta wahalshe ku da yaƙi.

56. Idan ba ku kore su ba, zan lalatar daku kamar yadda na shirya lalatar da su.”

Karanta cikakken babi L. Kid 33