Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 31:46-54 Littafi Mai Tsarki (HAU)

46. 'yan mata dubu goma sha shida (16,000).

47. Daga rabin kashi na jama'ar Isra'ila, Musa ya ɗauki ɗaya daga cikin hamsin na 'yan mata, da na dabbobi, ya ba Lawiyawan da suke lura da alfarwar sujada ta Ubangiji kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

48. Sai shugabannin da suka shugabanci rundunar yaƙin, suka zo wurin Musa.

49. Suka ce masa, “Mu barorinka mun ƙidaya mayaƙan da suke ƙarƙashin ikonmu, ba wanda ya ɓace daga cikinmu.

50. Mun kuwa kawo wa Ubangiji hadaya daga cikin abubuwan da kowannenmu ya samu, kayan ado na zinariya, da mundaye, da ƙawane da 'yan kunne, da duwatsun wuya, don yi wa kanmu kafara a gaban Ubangiji.”

51. Musa da Ele'azara firist, suka karɓi zinariya da kayan adon duka.

52. Dukan zinariya da shugabanni suka bayar hadaya ga Ubangiji, nauyinta ya kai shekel dubu goma sha shida da ɗari bakwai da hamsin (16,750).

53. Kowane soja ya kwashi ganimarsa.

54. Musa da Ele'azara firist kuwa, suka karɓi zinariya da shugabanni suka bayar, suka kai su cikin alfarwa ta sujada don ta zama abin tunawa da jama'ar Isra'ila a gaban Ubangiji.

Karanta cikakken babi L. Kid 31