Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 3:36-49 Littafi Mai Tsarki (HAU)

36. Aikin da aka danƙa wa 'ya'yan Merari shi ne lura da katakan alfarwar, da sanduna, da dirkoki, da kwasfa, da sauran abubuwa duka, da duk ayyukan da suka shafi waɗannan,

37. da kuma dirkoki na farfajiyar da ta kewaye wurin, da kwasfa da turaku da igiyoyinsu.

38. Waɗanda za su yi zango a gaban alfarwa ta sujada daga gabas, su ne Musa, da Haruna da 'ya'yansa maza, waɗanda aka danƙa musu tafiyar da aikin Wuri Mai Tsarki, da dukan aikin da za a yi wa Isra'ilawa. Banda su, duk wanda ya je kusa da wurin sai a kashe shi.

39. Dukan Lawiyawa waɗanda Musa da Haruna suka ƙidaya bisa ga iyalansu, bisa ga umarnin Ubangiji, tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba, mazaje dubu ashirin da dubu biyu ne (22,000).

40. Sai kuma Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙidaya dukan 'ya'yan fari maza na Isra'ilawa, tun daga wata ɗaya zuwa mai gaba, ka rubuta sunayensu.

41. Za ka keɓe mini Lawiyawa a maimakon 'ya'yan fari maza na Isra'ilawa. Dabbobin Lawiyawa za su zama nawa a maimakon dukan 'ya'yan farin dabbobin Isra'ilawa. Ni ne Ubangiji.”

42. Sai Musa ya ƙidaya 'ya'yan fari maza na Isra'ilawa, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

43. Jimillar 'ya'yan fari maza da aka ƙidaya bisa ga sunayensu tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba, mutum dubu ashirin da biyu, da ɗari biyu da saba'in da uku ne (22,273).

44. Ubangiji kuma ya yi magana da Musa, ya ce,

45. “Ka keɓe Lawiyawa a maimakon dukan 'ya'yan fari na Isra'ilawa. Dabbobin Lawiyawa kuma za su zama a maimakon 'ya'yan farin dabbobin Isra'ilawa. Lawiyawa kuwa za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.

46. 'Ya'yan fari maza na Isra'ilawa sun fi Lawiyawa da mutum ɗari biyu da saba'in da uku. Sai a fanshi wannan ragowa.

47. Ka karɓi shekel biyar a kan kowane mutum, bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi.

48. Sai ka ba da kuɗin fansar ga Haruna da 'ya'yansa maza.”

49. Musa kuwa ya karɓi kuɗin fansar waɗanda suka haura yawan Lawiyawa.

Karanta cikakken babi L. Kid 3