Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Yawan Lawiyawa da Aikinsu

1. Waɗannan su ne zuriyar Haruna da Musa lokacin da Ubangiji ya yi magana da Musa a bisa Dutsen Sinai.

2. Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Haruna, maza, Nadab ɗan fari, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar.

3. Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Haruna, maza, da aka naɗa firistoci domin su yi aikin firist.

4. Amma Nadab da Abihu sun mutu a gaban Ubangiji a jejin Sinai, a sa'ad da suka ƙona turare da haramtacciyar wuta. Sun mutu, ba su da 'ya'ya, saboda haka Ele'azara da Itamar suka yi aikin firist su kaɗai a zamanin mahaifinsu Haruna.

5. Ubangiji ya ce wa Musa,

6. “Kawo kabilar Lawiyawa kusa, ka sa su su yi aiki tare da Haruna, firist.

7. Sai su yi wa firistoci da dukan jama'a aiki a gaban alfarwa ta sujada.

8. Su za su lura da kayayyakin alfarwa ta sujada su kuma yi wa Isra'ilawa aiki.

9. Abin da Lawiyawa za su yi, shi ne su yi wa Haruna da 'ya'yansa aiki.

10. Ka sa Haruna da 'ya'yansa maza, su kula da aikinsu na firist, idan kuwa wani mutum dabam ya yi ƙoƙarin yin wannan aiki, to, za a kashe shi.”

11. Ubangiji kuma ya ce wa Musa,

12. “Ga shi, na ɗauki Lawiyawa daga cikin Isra'ilawa a maimakon kowane ɗan farin da ya buɗe mahaifa daga cikin mutanen Isra'ila. Lawiyawa za su zama nawa.

13. Gama 'yan fari duka nawa ne, tun daga ranar da na kashe 'ya'yan fari na ƙasar Masar, na keɓe wa kaina duk ɗan fari na Isra'ila, na mutum da na dabba. Za su zama nawa, ni ne Ubangiji.”

14. Ubangiji ya yi magana da Musa a jejin Sinai, ya ce masa

15. ya ƙidaya mazaje na kabilar Lawi bisa ga gidajen kakanninsu da iyalansu, tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba.

16. Haka Musa ya ƙidaya su bisa ga maganar Ubangiji, kamar yadda ya umarce shi.

17. Waɗannan su ne 'ya'yan Lawi, maza, bisa ga sunayensu, da Gershon, da Kohat, da Merari.

18. Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Gershon, maza, bisa ga iyalansu, Libni da Shimai.

19. Ga 'ya'yan Kohat, maza, bisa ga iyalansu, da Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel.

20. Ga kuma 'ya'yan Merari, maza, bisa ga iyalansu, da Mali da Mushi. Waɗannan su ne iyalan Lawi bisa ga gidajen kakanninsu.

21. Iyalin Libnawa, da na Shimaiyawa su ne iyalan Gershon.

22. Jimillarsa tun daga ɗa namiji mai wata ɗaya zuwa gaba, mutum dubu bakwai ne da ɗari biyar (7,500).

23. Iyalan Gershonawa za su yi zango a bayan alfarwar daga yamma.

24. Eliyasaf, ɗan Layel, shi ne shugaban gidan kakanninsa, Gershonawa.

25. 'Ya'yan Gershon, maza, su ne da aikin lura da alfarwa ta sujada da murfinta na ciki da na waje, da labulen ƙofar,

26. da labulen farfajiyar da yake kewaye da alfarwar, da bagade, da labulen ƙofar farfajiyar. Su za su lura da dukan aikin da ya shafi waɗannan abubuwa.

27. Iyalan Kohat su ne iyalin Amramawa, da na Izharawa, da na Hebronawa, da na Uzziyelawa. Waɗannan su ne iyalan Kohatawa.

28. Lissafin mazaje duka, tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba, su dubu takwas ne da ɗari shida (8,600).

29. Iyalan 'ya'yan Kohat za su kafa zangonsu a kudancin alfarwar.

30. Elizafan ɗan Uzziyel shi ne shugaban gidan kakanninsa, Kohatawa.

31. Aikinsu shi ne lura da akwatin alkawari, da tebur, da alkuki, da bagadai, da kayayyakin Wuri Mai Tsarki waɗanda firistoci suke aiki da su, da labule, da dukan aikin da ya shafi waɗannan abubuwa.

32. Ele'azara, ɗan Haruna, firist, shi zai shugabanci shugabannin Lawiyawa, shi ne kuma zai lura da waɗanda suke aiki a Wuri Mai Tsarki.

33. Iyalan Merari su ne iyalin Maliyawa, da na Mushiyawa. Waɗannan su ne iyalan Merari.

34. Yawan mazajensu duka da aka ƙidaya tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba, mutum dubu shida ne da ɗari biyu (6,200).

35. Shugaban gidan kakannin iyalan Merari kuwa shi ne Zuriyel, ɗan Abihail. Za su kafa zangonsu a arewacin alfarwar.

36. Aikin da aka danƙa wa 'ya'yan Merari shi ne lura da katakan alfarwar, da sanduna, da dirkoki, da kwasfa, da sauran abubuwa duka, da duk ayyukan da suka shafi waɗannan,

37. da kuma dirkoki na farfajiyar da ta kewaye wurin, da kwasfa da turaku da igiyoyinsu.

38. Waɗanda za su yi zango a gaban alfarwa ta sujada daga gabas, su ne Musa, da Haruna da 'ya'yansa maza, waɗanda aka danƙa musu tafiyar da aikin Wuri Mai Tsarki, da dukan aikin da za a yi wa Isra'ilawa. Banda su, duk wanda ya je kusa da wurin sai a kashe shi.

39. Dukan Lawiyawa waɗanda Musa da Haruna suka ƙidaya bisa ga iyalansu, bisa ga umarnin Ubangiji, tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba, mazaje dubu ashirin da dubu biyu ne (22,000).

An Fanshi 'Ya'yan Fari Maza

40. Sai kuma Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙidaya dukan 'ya'yan fari maza na Isra'ilawa, tun daga wata ɗaya zuwa mai gaba, ka rubuta sunayensu.

41. Za ka keɓe mini Lawiyawa a maimakon 'ya'yan fari maza na Isra'ilawa. Dabbobin Lawiyawa za su zama nawa a maimakon dukan 'ya'yan farin dabbobin Isra'ilawa. Ni ne Ubangiji.”

42. Sai Musa ya ƙidaya 'ya'yan fari maza na Isra'ilawa, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

43. Jimillar 'ya'yan fari maza da aka ƙidaya bisa ga sunayensu tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba, mutum dubu ashirin da biyu, da ɗari biyu da saba'in da uku ne (22,273).

44. Ubangiji kuma ya yi magana da Musa, ya ce,

45. “Ka keɓe Lawiyawa a maimakon dukan 'ya'yan fari na Isra'ilawa. Dabbobin Lawiyawa kuma za su zama a maimakon 'ya'yan farin dabbobin Isra'ilawa. Lawiyawa kuwa za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.

46. 'Ya'yan fari maza na Isra'ilawa sun fi Lawiyawa da mutum ɗari biyu da saba'in da uku. Sai a fanshi wannan ragowa.

47. Ka karɓi shekel biyar a kan kowane mutum, bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi.

48. Sai ka ba da kuɗin fansar ga Haruna da 'ya'yansa maza.”

49. Musa kuwa ya karɓi kuɗin fansar waɗanda suka haura yawan Lawiyawa.

50. Kuɗin da ya karɓa daga 'ya'yan fari na Isra'ilawa da suka haura yawan Lawiyawa shekel dubu ɗaya da ɗari uku da sittin da biyar (1,365) bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi.

51. Musa kuwa ya ba Haruna da 'ya'yansa maza kuɗin fansa bisa ga maganar Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.