Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 29:15-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. da humushin garwa kuma tare da kowane ɗan rago.

16. Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda yin hadaya don zunubi. Banda waɗannan hadayu kuma za a riƙa yin hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.

17. A rana ta biyu ta idin za a miƙa bijimai goma sha biyu, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dukan dabbobin su zama marasa lahani.

18. Za a kuma miƙa hadaya ta gari da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar.

19. Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gari, da hadayarsu ta sha.

20. A rana ta uku ta idin za a miƙa bijimai goma sha ɗaya, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani.

21. Za a kuma miƙa hadaya ta gari da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar.

22. Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.

23. A rana ta huɗu ta idin za a miƙa bijimai goma, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani.

24. Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar.

25. Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.

26. A rana ta biyar ta idin za a miƙa bijimai tara, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani.

27. Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar.

Karanta cikakken babi L. Kid 29