Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 29:12-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. A rana ta goma sha biyar ga watan bakwai za a yi tsattsarkan taro domin yin sujada, ba za a yi aiki ba. Su kiyaye idin da girmama Ubangiji har kwana bakwai.

13. Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da 'yan bijimai goma sha uku, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin nan su zama marasa lahani.

14. Tare da dabbobin za a miƙa hadaya ta lallausan gāri wanda aka kwaɓa da mai. Za a miƙa gāri humushi uku na garwa tare da kowane bijimi, da gāri humushi biyu na garwa tare da kowane rago,

15. da humushin garwa kuma tare da kowane ɗan rago.

16. Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda yin hadaya don zunubi. Banda waɗannan hadayu kuma za a riƙa yin hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.

17. A rana ta biyu ta idin za a miƙa bijimai goma sha biyu, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dukan dabbobin su zama marasa lahani.

18. Za a kuma miƙa hadaya ta gari da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar.

Karanta cikakken babi L. Kid 29