Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 27:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai 'ya'yan Zelofehad, mata, ɗan Hefer ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manassa, ɗan Yusufu, suka tafi ƙofar alfarwa ta sujada. Sunayen 'ya'ya, matan ke nan, Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza.

2. Da suka tafi, suka tsaya a gaban Musa da Ele'azara, firist, da gaban shugabanni, da dukan taron jama'a, suka ce,

3. “Mahaifinmu ya rasu cikin jeji. Ba ya cikin ƙungiyar Kora wadda ta tayar wa Ubangiji. Ya rasu saboda alhakin zunubinsa. Ga shi, ba shi da 'ya'ya maza.

4. Don me za a tsame sunan mahaifinmu daga cikin zuriyar iyalinsa saboda ba shi da ɗa? In ka yarda, muna roƙonka ka ba mu gādo tare da 'yan'uwan mahaifinmu.”

5. Musa ya kai maganarsu a gaban Ubangiji.

6. Ubangiji ya ce wa Musa,

7. “Maganar 'ya'yan Zelofehad, mata, daidai ce, saika ba su gādo tare da 'yan'uwan mahaifinsu. Za ka sa gādon mahaifinsu ya zama nasu.

8. Sai kuma ka shaida wa Isra'ilawa, ka ce, ‘Idan mutum ya rasu ba shi da ɗa,sai 'yarsa ta ci gādonsa.

9. Idan kuwa ba shi da 'ya, sai a ba 'yan'uwansa gādonsa.

10. Idan kuma ba shi da 'yan'uwa, sai a ba 'yan'uwan mahaifinsa gādonsa.

11. Idan kuma ba shi da su, sai a ba danginsa na kusa su mallaka, wannan zai zama umarni da ka'ida ga Isra'ilawa kamar yadda ni, Ubangiji na umarce ka.’ ”

12. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Hau bisa kan Dutsen Abarim, ka dubi ƙasa wadda na ba Isra'ilawa.

Karanta cikakken babi L. Kid 27