Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 25:3-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ta haka Isra'ilawa suka shiga bautar gumakan Ba'al na Feyor. Sai Ubangiji ya husata da Isra'ilawa.

4. Ya ce wa Musa, “Ɗauki sugabannin jama'a, ka rataye su a rana a gabana don in huce daga fushin da nake yi da Isra'ilawa.”

5. Musa kuwa ya ce wa alƙalan Isra'ilawa, “Kowa ya kashe mutanensa da suka shiga bautar gumakan Ba'al-feyor.”

6. Sai ga wani Ba'isra'ile ya taho da wata mace, Bamadayaniya, ya kai ta alfarwarsa ƙiriƙiri a gaban Musa da dukan taron jama'ar Isra'ila a sa'ad da suke kuka a ƙofar alfarwa ta sujada.

7. Finehas ɗan Ele'azara, wato jikan Haruna, firist, ya gani, sai ya tashi daga cikin taron, ya ɗauki mashi.

8. Ya bi Ba'isra'ilen, har zuwa ƙuryar alfarwar, ya soke dukansu biyu, Ba'isra'ilen da macen, har ya sha zarar macen. Da haka aka tsai da annoba daga Isra'ilawa.

9. Duk da haka annobar ta kashe mutane dubu ashirin da dubu huɗu (24,000).

Karanta cikakken babi L. Kid 25