Ya bi Ba'isra'ilen, har zuwa ƙuryar alfarwar, ya soke dukansu biyu, Ba'isra'ilen da macen, har ya sha zarar macen. Da haka aka tsai da annoba daga Isra'ilawa.