Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 25:10-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

11. “Finehas ɗan Ele'azara, wato jikan Haruna, firist, ya kawar da fushina daga Isra'ilawa saboda ya yi kishi irin nawa a gabansu, don haka ban shafe Isra'ilawa saboda kishina ba.

12. Domin haka ina yi masa alkawarin da ba zai ƙare ba.

13. Alkawarin zai zama nasa da na zuriyarsa, wato alkawarin zama firist din din din, domin ya yi kishi saboda Allahnsa. Ya kuwa yi kafara domin Isra'ilawa.”

14. Sunan Ba'isra'ilen da aka kashe tare da Bamadayaniyar, Zimri ɗan Salu, shi ne shugaban gidan Saminawa.

15. Sunan Bamadayaniya kuwa, Kozbi, 'yar Zur. Shi ne shugaban mutanen gidan ubansa a Madayana.

16. Ubangiji kuma ya umarci Musa, ya ce,

17. “Ku fāɗa wa Madayanawa ku hallaka su.

18. Gama sun dame ku da makircinsu da suka yaudare ku a kan al'amarin Feyor da na Kozbi 'yar'uwarsu, 'yar shugaban Madayana, wadda aka kashe a ranar da aka yi annoba a Feyor.”

Karanta cikakken babi L. Kid 25