Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 24:9-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Al'ummar tana kama da ƙaƙƙarfan zakiSa'ad da yake barci, ba wanda zai yi ƙarfin hali ya tashe shi.Duk wanda ya sa muku albarka zai sami albarka,Duk wanda ya sa muku la'ana zai sami la'ana.”

10. Sai Balak ya husata da Bal'amu, ya tafa hannunsa ya ce wa Bal'amu, “Na kirawo ka don ka la'anta maƙiyana, amma ga shi, har sau uku kana sa musu albarka.

11. Yanzu sai ka tafi abinka. Hakika,na ce zan ɗaukaka ka, amma ga shi, Ubangiji ya hana maka ɗaukakar.”

12. Sai Bal'amu ya ce wa Balak, “Ashe, ban faɗa wa manzanninka waɗanda ka aiko gare ni ba?

13. Na ce, ‘Ko da Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan iya in zarce maganar Ubangiji ba, in aikata nagarta ko mugunta bisa ga nufin kaina.’ Abin da Ubangiji ya faɗa shi ne zan faɗa.”

14. Bal'amu ya ce wa Balak, “Yanzu fa, zan koma wurin mutanena. Ka zo in sanar maka da abinda mutanen nan za su yi wa mutanenka nan gaba.”

15. Sai ya hurta jawabinsa, ya ce,“Faɗar Bal'amu ɗan Beyor,Faɗar mutumin da idonsa take buɗe,

Karanta cikakken babi L. Kid 24