Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 24:3-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Sai ya yi annabcinsa, ya ce.“Faɗar Bal'amu ɗan Beyor,Faɗar mutumin da idonsa take a buɗe.

4. Faɗar wanda yake jin faɗar Allah,Shi wanda yake ganin wahayin Maɗaukaki,Yana durƙushe, amma idanunsa a buɗe suke.

5. Alfarwan Isra'ilawa suna da kyan gani!

6. Kamar dogon jerin itatuwan dabino,Kamar gonaki a gefen kogi,Kamar itatuwan aloyes da Ubangiji ya dasa,Kamar kuma itatuwan al'ul a gefen ruwaye.

7. Sojojin Isra'ilawa za su sa al'ummai rawar jiki;Za su yi mulkin jama'a mai yawaSarkinsu zai fi Agag girma,Za a ɗaukaka mulkinsa.

8. Allah ne ya fisshe su daga Masar,Kamar kutunkun ɓauna yake a gare su,Yakubu zai cinye maƙiyansa,Zai kakkarya ƙasusuwansu, ya mummurɗe kibansu.

9. Al'ummar tana kama da ƙaƙƙarfan zakiSa'ad da yake barci, ba wanda zai yi ƙarfin hali ya tashe shi.Duk wanda ya sa muku albarka zai sami albarka,Duk wanda ya sa muku la'ana zai sami la'ana.”

10. Sai Balak ya husata da Bal'amu, ya tafa hannunsa ya ce wa Bal'amu, “Na kirawo ka don ka la'anta maƙiyana, amma ga shi, har sau uku kana sa musu albarka.

11. Yanzu sai ka tafi abinka. Hakika,na ce zan ɗaukaka ka, amma ga shi, Ubangiji ya hana maka ɗaukakar.”

Karanta cikakken babi L. Kid 24