Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 24:13-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Na ce, ‘Ko da Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan iya in zarce maganar Ubangiji ba, in aikata nagarta ko mugunta bisa ga nufin kaina.’ Abin da Ubangiji ya faɗa shi ne zan faɗa.”

14. Bal'amu ya ce wa Balak, “Yanzu fa, zan koma wurin mutanena. Ka zo in sanar maka da abinda mutanen nan za su yi wa mutanenka nan gaba.”

15. Sai ya hurta jawabinsa, ya ce,“Faɗar Bal'amu ɗan Beyor,Faɗar mutumin da idonsa take buɗe,

16. Faɗar wanda yake jin faɗar Allah,Wanda ya san hikimar Maɗaukaki,Wanda yake ganin wahayin Mai Iko Dukka,Yana durƙurshe, amma idanunsa a buɗe suke.

17. Ina ganinsa, amma ba yanzu ba,Ina hangensa, amma ba kusa ba.Tauraro zai fito daga cikin Yakubu,Kandiri zai fito daga cikin Isra'ila,Zai ragargaje goshin Mowabawa,Zai kakkarya 'ya'yan Shitu duka.

18. Za a mallaki Edom,Hakka kuma za a mallaki Seyir abokiyar gābanta,Isra'ila za ta gwada ƙarfi.

19. Yakubu zai yi mulki,Zai hallaka waɗanda suka ragu cikin birni.”

20. Sai ya dubi Amalek, ya hurta jawabinsa, ya ce,“Amalek na fari ne cikin al'ummai,amm ƙarshensa hallaka ne.”

21. Sai kuma ya dubi Keniyawa, ya hurta jawabinsa, ya ce,“Wurin zamanku mai ƙarƙo ne,Gidajenku kuma suna cikin duwatsu.

22. Duk da haka za a lalatar da Keniyawa.Har yaushe za ku zama bayin Assuriyawa?”

Karanta cikakken babi L. Kid 24