Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 24:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da Bal'amu ya gane Ubangiji yana jin daɗin sa wa Isra'ilawa albarka bai tafi neman shawara kamar dā ba, sai ya fuskanci jeji,

2. ya ta da idanunsa ya ga Isra'ilawa sun yi zango kabila kabila. Sai Ruhun Allah kuwa ya sauko masa.

3. Sai ya yi annabcinsa, ya ce.“Faɗar Bal'amu ɗan Beyor,Faɗar mutumin da idonsa take a buɗe.

4. Faɗar wanda yake jin faɗar Allah,Shi wanda yake ganin wahayin Maɗaukaki,Yana durƙushe, amma idanunsa a buɗe suke.

5. Alfarwan Isra'ilawa suna da kyan gani!

Karanta cikakken babi L. Kid 24