Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 23:14-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Ya kuwa kai shi saurar Zofim a bisa Dutsen Fisga. Sa'an nan ya gina bagadai bakwai, ya miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.

15. Sai Bal'amu ya ce wa Balak, “Tsaya nan kusa da hadayarka ta ƙonawa, ni kuwa in tafi in sadu da Ubangiji a can.”

16. Ubangiji kuwa ya sadu da Bal'amu ya sa masa magana a baka, ya ce, “Koma wurin Balak ka faɗa masa abin da na faɗa maka.”

17. Sai Bal'amu ya koma wurin Balak ya same shi yana tsaye kusa da hadayarsa ta ƙonawa tare da dattawan Mowab. Balak kuwa ya ce masa, “Me Ubangiji ya faɗa?”

18. Sai Bal'amu ya faɗi jawabinsa, ya ce,“Tashi, Balak, ka ji,Ka kasa kunne gare ni, ya ɗan Ziffor.

19. Allah ba kamar mutum ba ne, da zai yi ƙarya,Ba kuwa ɗan mutum ba ne, da zai tuba.Zai cika dukan abin da ya alkawarta,Ya hurta, ya kuwa cika.

20. Ga shi, an umarce ni in sa albarka.Ya sa albarka, ba zan iya janye ta ba.

21. Bai ga mugunta ga Yakubu ba,Bai kuma ga wahala a Isra'ilawa ba.Ubangiji Allahnsu yana tare da su,Suna sowar murna domin shi sarkinsu ne.

22. Allah ne ya fisshe shi daga Masar,Ya yi yaƙi dominsu kamar kutunkun ɓauna.

23. Ba wata maitar da za ta cuci Yakubu,Ba kuwa sihirin da zai cuci Isra'ilawa.Yanzu za a ce, ‘Duba irin abin da Allah ya yi domin Yakubu, wato Isra'ilawa!’

24. Ga shi, jama'ar Isra'ila tana kama da ƙaƙƙarfan zaki,Ba zai kwanta ba sai ya cinye ganimarsa.Ya lashe jinin waɗanda ya kashe.”

25. Sai Balak ya ce wa Bal'amu, “Kada ka la'anta su, kada kuma ka sa musu albarka.”

26. Bal'amu kuwa ya amsa wa Balak, ya ce, “Ban faɗa maka ba, duk abin da Ubangiji ya faɗa, shi ne zan yi?”

Karanta cikakken babi L. Kid 23