Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 23:13-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sai Balak ya ce masa, “Zo, mu tafi wani wuri inda za ka gan su. Waɗanda suka fi kusa kaɗai ne za ka gani, amma ba za ka iya ganinsu duka ba. Ka la'anta mini su daga can.”

14. Ya kuwa kai shi saurar Zofim a bisa Dutsen Fisga. Sa'an nan ya gina bagadai bakwai, ya miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.

15. Sai Bal'amu ya ce wa Balak, “Tsaya nan kusa da hadayarka ta ƙonawa, ni kuwa in tafi in sadu da Ubangiji a can.”

16. Ubangiji kuwa ya sadu da Bal'amu ya sa masa magana a baka, ya ce, “Koma wurin Balak ka faɗa masa abin da na faɗa maka.”

17. Sai Bal'amu ya koma wurin Balak ya same shi yana tsaye kusa da hadayarsa ta ƙonawa tare da dattawan Mowab. Balak kuwa ya ce masa, “Me Ubangiji ya faɗa?”

18. Sai Bal'amu ya faɗi jawabinsa, ya ce,“Tashi, Balak, ka ji,Ka kasa kunne gare ni, ya ɗan Ziffor.

19. Allah ba kamar mutum ba ne, da zai yi ƙarya,Ba kuwa ɗan mutum ba ne, da zai tuba.Zai cika dukan abin da ya alkawarta,Ya hurta, ya kuwa cika.

20. Ga shi, an umarce ni in sa albarka.Ya sa albarka, ba zan iya janye ta ba.

Karanta cikakken babi L. Kid 23