Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 22:34-41 Littafi Mai Tsarki (HAU)

34. Sai Bal'amu ya ce wa mala'ikan Ubangiji, “Na yi zunubi, gama ban sa ka tsaya a hanya don ka tarye ni ba. Yanzu fa, idan ka ga mugun abu ne, to, sai in koma.”

35. Ubangiji kuwa ya ce wa Bal'amu, “Tafi tare da mutanen, amma abin da na faɗa maka shi kaɗai za ka faɗa.” Sai Bal'amu ya tafi tare da dattawan Balak.

36. Sa'ad da Balak ya ji Bal'amu ya zo, sai ya fito ya tarye shi a Ar, wato wani birni a bakin Kogin Arnon, a kan iyakar Mowab.

37. Sai Balak ya ce wa Bal'amu, “Ashe, ban aika a kirawo ka ba? Me ya sa ba ka zo wurina ba, sai yanzu? Ko ban isa in ɗaukaka ka ba ne?”

38. Bal'amu ya amsa wa Balak ya ce, “To, ai, ga shi, na zo yanzu! Ina da wani ikon yin wata magana ne? Maganar da Allah ya sa a bakina, ita zan faɗa, tilas.”

39. Sai Bal'amu ya tafi tare da Balak suka je Kiriyat-huzot.

40. Can Balak ya yi hadaya da shanu da tumaki, ya kuwa aika wa Bal'amu da dattawan da suke tare da shi.

41. Kashegari, sai Balak ya ɗauki Bal'amu ya kai shi kan Bamotba'al, daga can ya ga rubu'in mutanen.

Karanta cikakken babi L. Kid 22