Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 22:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Isra'ilawa suka kama tafiya, suka yi zango a filayen Mowab a hayin Urdun daura da Yariko.

2. Balak ɗan Ziffor ya ga abin da Isra'ilawa suka yi wa Amoriyawa.

3. Sai Mowabawa suka firgita ƙwarai saboda yawan mutanen. Tsoron Isra'ilawa ya kama su.

4. Mowabawa kuwa suka ce wa dattawan Madayanawa, “Yanzun nan wannan taro zai lashe dukan abin da yake kewaye da mu kamar yadda sā yakan lashe ciyawar saura.” Don haka Balak ɗan Ziffor wanda yake sarautar Mowab a lokacin,

5. ya aiki manzanni zuwa wurin Bal'amu ɗan Beyor a Fetor, a ƙasar danginsa, wadda take kusa da kogin, su kirawo shi, su ce, “Ga mutane sun fito daga ƙasar Masar, sun mamaye ƙasar, ga shi, suna zaune daura da ni.

6. Ina roƙonka, ka zo yanzu, ka la'anta mini mutanen nan, gama sun fi ƙarfina, ko ya yiwu in ci su, in kore su daga ƙasar, gama na sani duk wanda ka sa wa albarka zai albarkatu,wanda kuwa ka la'anta, zai la'antu.”

7. Dattawan Mowab da na Madayana suka ɗauki kafin alkalami suka tafi wurin Bal'amu suka faɗa masa saƙon Balak.

8. Ya ce musu, “Ku kwana a nan, ni kuwa zan shaida muku abin da Ubangiji zai faɗa mini.” Sai dattawan Mowab suka zauna wurin Bal'amu.

9. Allah kuwa ya zo wurin Bal'amu ya ce masa, “Suwane ne mutanen da suke tare da kai?”

10. Sai Bal'amu ya ce wa Allah, “Ai, Balak ne ɗan Ziffor, Sarkin Mowab, ya aiko ya ce mini,

11. ‘Ga jama'a sun fito daga Masar, sun mamaye ƙasar, ka zo, ka la'anta mini su, watakila zan iya yin yaƙi da su, in kore su!’ ”

12. Allah kuwa ya ce wa Bal'amu, “Ba za ka tafi tare da su ba, ba kuwa za ka la'anta su ba, gama albarkatattu ne su.”

13. Da safe Bal'amu ya tashi, ya ce wa dattawan Balak, “Ku koma ƙasarku, gama Ubangiji bai yarda mini in tafi tare da ku ba.”

14. Domin haka dattawan Mowab suka tashi, suka koma wurin Balak, suka ce masa, “Bal'amu bai yarda ya biyo mu ba.”

15. Sai Balak ya sāke aiken dattawa da yawa masu daraja fiye da na dā.

Karanta cikakken babi L. Kid 22