Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 21:17-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Sai Isra'ilawa suka raira waƙa, suka ce,“Rijiya, ki ɓuɓɓugo da ruwaMu kuwa za mu raira waƙa mu gaishe ta!

18. Rijiyar da hakimai suka haƙa,Shugabannin jama'a suka haƙa,Da sandan sarauta,Da kuma sandunansu.”Daga cikin jejin suka tafi har zuwa Mattana.

19. Daga Mattana suka tafi Nahaliyel suka tafi Bamot.

20. Daga Bamot kuma suka tafi kwarin da yake a ƙasar Mowab wajen ƙwanƙolin Dutsen Fisga wanda yake fuskantar hamada.

21. Mutanen suka aiki manzanni zuwa wurin Sihon, Sarkin Amoriyawa, suka ce masa,

22. “Ka yarda mana mu ratsa ta ƙasarka, ba za mu ratsa ta cikin gonaki, ko cikin gonakin inabi ba, ba kuwa za mu sha ruwan rijiyarka ba, gwadaben sarki za mu bi sosai, har mu fita daga karkararka.”

23. Amma Sihon bai yarda wa Isra'ilawa su ratsa ta karkararsa ba. Sai ya tattara mazajensa, suka fita don su yi yaƙi da Isra'ilawa a jejin. Suka tafi Yahaza suka yi yaƙi da Isra'ilawa.

24. Isra'ilawa kuwa suka karkashe su da takobi, suka mallaki ƙasarsa tun daga Kogin Arnon zuwa Kogin Yabbok, har zuwa kan iyakar Ammonawa, gama Yahaza ita ce kan iyakar Ammonawa.

25. Isra'ilawa kuwa suka ci dukan waɗannan birane, suka zauna a biranen Amoriyawa, wato a Heshbon da ƙauyukanta duka.

26. Gama Heshbon ita ce birnin Sihon,Sarkin Amoriyawa, wanda ya yi yaƙi da Sarkin Mowab na dā. Ya ƙwace ƙasarsa duka daga hannunsa har zuwa Kogin Arnon.

27. Domin haka mawaƙa sukan ce,“Ku zo Heshbon, bārin sarki Sihon!Muna so mu ga an sāke gina an kuma fanso shi.

28. Gama sojojin Sihon sun shiga kamar wuta,A wannan birni na Heshbon,Sun cinye Ar ta Mowab,Ta murƙushe tuddan Arnon.

29. Kaitonku, ku mutanen Mowab!Ku masu sujada ga Kemosh kun lalace!Gumakanku sun sa mutane su zama 'yan gudun hijira,Mata kuwa, Sihon, Sarkin Amoriyawa ya kama su.

Karanta cikakken babi L. Kid 21