Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 20:11-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Musa kuwa ya ɗaga hannu, ya bugi dutsen sau biyu da sandansa, sai ruwa mai yawa ya yi ta kwararowa. Taron jama'a tare da garkunansu suka sha.

12. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa da Haruna, “Tun da yake ba ku gaskata ni ba, ba ku kuwa ɗaukaka ni a idon Isra'ilawa ba, to, ba za ku kai taron jama'ar nan a ƙasar da na ba su ba.”

13. Wannan ya faru ne a Meriba inda mutanen Isra'ila suka yi wa Ubangiji gunaguni, inda shi kuma ya nuna musu shi mai tsarki ne.

14. Sai Musa ya aika manzanni daga Kadesh zuwa wurin Sarkin Edom, su ce masa, “In ji ɗan'uwanka, Isra'ila, ka dai san dukan wahalar da ta same mu,

15. yadda kakanninmu suka gangara zuwa Masar, suka zauna a can da daɗewa, da yadda Masarawa suka wahalshe mu, mu da kakanninmu.

16. Sa'ad da muka yi kuka ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya ji kukanmu, ya aiko mala'ikansa, ya fisshe mu daga Masar. Ga mu nan a Kadesh, garin da yake kan iyakar ƙasarka.

17. Ka yarda mana mu ratsa ƙasarka, ba za mu bi ta cikin gona, ko gonar inabi ba, ba kuwa za mu sha ruwan rijiyarka ba. Mu dai za mu bi gwadaben sarki, ba za mu kauce dama ko hagu ba, har mu wuce ƙasarka.”

18. Amma Edomawa suka ce masa, “Ba za ku ratsa ta ƙasarmu ba! Idan kuwa kun ce za ku gwada, za mu fita mu ci ku da yaƙi.”

19. Amma mutanen Isra'ila suka amsa musu suka ce, “Ai, za mu bi gwadabe ne kawai, idan kuwa mu da dabbobinmu mun sha ruwanku, sai mu biya, mu dai, a yardar mana mu wuce kawai.”

20. Amma Edomawa suka sāke cewa, “Ba mu yarda ba.” Sai suka fito da runduna mai yawa su yi yaƙi da su.

21. Da haka Edomawa suka hana Isra'ilawa ratsa ƙasarsu. Sai Isra'ilawa suka kauce musu.

Karanta cikakken babi L. Kid 20