Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 17:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya yi magana da Musa ya ce,

2. “Ka faɗa wa Isra'ilawa su ba ka sanduna, sanda guda daga kowane shugaban gidan kakanninsu, sanduna goma sha biyu ke nan. Ka rubuta sunan kowane mutum a sandansa.

3. Ka rubuta sunan Haruna a kan sandan Lawi, gama akwai sanda guda domin kowane gidan kakanninsu.

4. Sai ka ajiye su a alfarwa ta sujada a gaban akwatin alkawari, inda nakan sadu da kai.

5. Mutumin da sandansa ya yi toho, shi ne na zaɓa, da haka zan sa gunagunin da Isra'ilawa suke yi a kaina ya ƙare.”

6. Musa kuwa ya yi magana da Isra'ilawa. Sai dukan shugabanninsu suka ba shi sanda ɗaya ɗaya, sanda ɗaya daga kowane shugaba bisa ga gidajen kakanninsu, sanduna goma sha biyu ke nan. Sandan Haruna yana cikin sandunan.

7. Sai Musa ya ajiye sandunan a gaban Ubangiji cikin alfarwa ta sujada.

Karanta cikakken babi L. Kid 17