Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 15:14-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Idan baƙon da yake baƙunci a cikinsu ko ko wane ne da yake tare da su a dukan zamanansu, yana so ya ba da hadayar da akan yi da wuta don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, sai ya yi kamar yadda suke yi.

15. Ka'ida ɗaya ce domin taron jama'a da kuma baƙin da yake zaune tare da su. Ka'ida ce madawwamiya a dukan zamanansu. Kamar yadda suke a gaban Ubangiji, haka kuma baƙon da yake baƙunci a cikinsu yake.

16. Ka'ida ɗaya ce umarni kuma ɗaya ne domin su da baƙin da yake baƙunci a cikinsu.

17. Ubangiji ya ba Musa

18. waɗannan ka'idodi domin Isra'ilawa su kiyaye a ƙasar da zai ba su.

19. Sa'ad da suke cin amfaninta, sai su miƙa hadaya ta ɗagawa ga Ubangiji.

20. Daga cikin ɓarzajjen hatsinsu na nunan fari sai su yi wainar da za su ɗaga don yin hadaya da amfanin masussuka.

21. Daga cikin ɓarzajjen hatsinsu na nunan fari, sai su miƙa wa Ubangiji hadaya ta ɗagawa a dukan zamanansu.

22. Amma idan sun yi kuskure, ba su kiyaye dukan umarnan nan waɗanda Ubangiji ya faɗa wa Musa ba,

23. wato duk dai abin da ubangiji ya umarta ta bakin Musa tun daga ranar da Ubangiji ya ba da umarnan, har zuwa dukan zamanansu,

24. idan jama'a sun yi kuskure da rashin sani, sai su miƙa maraƙi don yin hadaya ta ƙonawa don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Su kuma ba da hadaya ta gari, da hadaya ta sha tare da maraƙin bisa ga ka'idar. Za su kuma miƙa bunsuru ɗaya na yin hadaya don zunubi.

25. Firist kuwa zai yi kafara domin dukan jama'ar Isra'ilawa, za a kuwa gafarta musu kuskuren, domin sun kawo hadaya ta ƙonawa da hadaya don zunubi ga Ubangiji saboda kuskurensu.

26. Za a gafarta wa dukan taron jama'ar Isra'ilawa da baƙon da yake baƙunci a cikinsu, kuskuren da suka yi.

27. Idan bisa ga kuskure wani mutum ya yi zunubi, sai ya ba da 'yar akuya bana ɗaya ta yin hadaya don zunubi.

28. Firist kuwa zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mutumin da ya yi kuskuren, gama ya yi zunubi ba da saninsa ba, za a kuwa gafarta masa.

29. Ka'idarsu ɗaya ce a kan wanda ya yi kuskure, ko Ba'isra'ile ne, ko baƙon da yake baƙunci a cikinsu.

30. Amma mutumin da ya yi laifi da gangan, ko shi ɗan ƙasa ne, ko kuma baƙo ne, ya sāɓi Ubangiji, sai a kashe shi,

31. gama ya raina maganar Ubangiji, ya karya umarninsa. Hakika za a kashe mutumin nan, alhakin zunubinsa, yana wuyansa.

Karanta cikakken babi L. Kid 15