Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 14:22-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. dukan mutanen da suka ga ɗaukakata da alamuna waɗanda na aikata a Masar, da kuma a jejin, suka kuwa jarraba ni har sau goma, ba su kuma yi biyayya da maganata ba,

23. ba za su ga ƙasar da na rantse zan ba kakanninsu ba. Duk waɗanda suka raina ni, ba za su ga ƙasar ba,

24. sai dai bawana Kalibu da yake ruhunsa dabam ne, gama ya bi ni sosai.

25. Yanzu fa, tun da yake Amalekawa da Kan'aniyawa suna zaune a kwarin, gobe sai ku juya ku nufi wajen jejin ta hanyar Bahar Maliya.”

26. Ubangiji kuma ya ce wa Musa da Haruna,

27. “Har yaushe wannan mugun taron jama'a zai yi ta gunaguni a kaina? Na ji gunagunin da Isra'ilawa suka yi a kaina.

28. Sai ka faɗa musu cewa, ‘Ni Ubangiji na rantse da zatina, abin da kuka sanar da ni zan yi muku.

29. Gawawwakin waɗanda suka yi gunaguni a kaina za su fādi cikin jejin nan. Dukan waɗanda aka ƙidaya, tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba,

30. ba wanda zai shiga ƙasar da na rantse ta zama wurin zamanku, sai Kalibu, ɗan Yefunne, da Joshuwa ɗan Nun.

31. Amma 'yan ƙanananku, waɗanda kuka ce za su zama ganima, su ne zan kai su cikin ƙasar, za su san ƙasar da kuka raina.

32. Amma ku, gawawwakinku za su fāɗi a jejin.

33. 'Ya'yanku za su yi yawo a jeji shekara arba'in, za su sha wahala saboda rashin bangaskiyarku, har mutuminku na ƙarshe ya mutu a jejin.

Karanta cikakken babi L. Kid 14