Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 13:24-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Aka kira wurin Kwarin Eshkol, wato “nonon inabi,” saboda nonon inabi wanda 'yan leƙen ƙasa suka yanko a wurin.

25. Bayan sun yi kwana arba'in suna leƙen asirin ƙasar, sai suka komo.

26. Suka zo wurin Musa, da Haruna, da dukan taron jama'ar Isra'ila a jejin Faran a Kadesh. Suka faɗa musu labarin tafiyarsu, suka kuma nuna musu amfanin ƙasar da suka kawo.

27. Suka ce wa Musa, “Mun tafi ƙasar da ka aike mu, ƙasar tana da yalwar abinci, ga kuma amfanin ƙasar.

28. Amma mazaunan ƙasar ƙarfafa ne, biranenta kuma manya ne, masu garu, banda wannan kuma, mun ga Anakawa a can.

29. Amalekawa suna zaune a Negeb, Hittiyawa kuwa, da Yebusiyawa, da Amoriyawa suna zaune a ƙasar tuddai, Kan'aniyawa suna zaune kusa da teku, da kuma kusa da Kogin Urdun.”

30. Amma Kalibu ya sa mutane su yi shiru a gaban Musa, ya ce, “Bari mu tafi nan da nan mu mallaki ƙasar, gama za mu iya cinta.”

31. Sai mutanen da suka tafi tare da shi suka amsa suka ce, “Ba za mu iya haurawa, mu kara da mutanen ba, gama sun fi mu ƙarfi.”

32. Haka suka kawo wa 'yan'uwansu, Isra'ilawa, mugun rahoton ƙasa wadda suka leƙi asirinta, suka ƙara da cewa, “Ƙasar da muka ratsa cikinta domin mu leƙi asirinta, tana cinye waɗanda suke zaune a cikinta, dukan mutane kuma da muka gani a cikinta ƙatti ne.

33. Mun kuma ga manyan mutane a can, wato mutanen Anakawa da suka fito daga Nefilawa. Sai muka ga kanmu kamar fara ne kawai, haka kuwa muke a gare su.”

Karanta cikakken babi L. Kid 13