Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 12:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Maryamu da Haruna suka zargi Musa saboda mace, Bahabashiya, wadda ya aura.

2. Suka ce, “Da Musa kaɗai ne, Ubangiji ya yi magana, bai yi magana da mu kuma ba?” Ubangiji kuwa ya ji.

3. (Musa dai mai tawali'u ne ƙwarai, fiye da kowane mutum a duniya.)

4. Farat ɗaya sai Ubangijiya ce wa Musa, da Haruna, da Maryamu, “Ku uku, ku tafi zuwa alfarwa ta sujada.” Sai su uku suka tafi.

5. Ubangiji kuwa ya zo cikin al'amudin girgije, ya tsaya a ƙofar alfarwar, ya yi kira, “Haruna! Maryamu!” Su biyu fa suka gusa gaba.

6. Ya ce, “Ku ji abin da zan faɗa! Idan akwai annabawa a cikinku, nakan bayyana gare su cikin wahayi, in kuma yi magana da su ta cikin mafarki.

7. Ba haka nake magana da bawana Musa ba, na sa shi ya lura da dukkan jama'ata Isra'ila.

8. Nakan yi magana da shi fuska da fuska a sarari, ba a duhunce ba. Yakan kuma ga zatina. Me ya sa ba ku ji tsoron zargin bawana Musa ba?”

9. Ubangiji kuwa ya husata da su, ya rabu da su.

Karanta cikakken babi L. Kid 12