Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 11:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da Ubangiji ya ji gunagunin da mutanen suke yi saboda wahalarsu, sai ya husata ƙwarai, wutarsa ta yi ta ci a cikinsu har ta ƙone wani gefe na zangon.

2. Sai mutanen suka yi ta yi wa Musa kuka, Musa kuwa ya yi addu'a ga Ubangiji, wutar kuwa ta mutu.

3. Aka sa wa wurin suna Tabera, wato matoya, domin wutar Ubangiji ta yi ƙuna a cikinsu.

4. Tattarmukan da suke cikinsu kuwa suka faye kwaɗayin nama, har Isra'ilawa ma da kansu suka fara gunaguni suna cewa, “Wa zai ba mu nama mu ci?

5. Mun tuna da kifin da muka ci kyauta a Masar, da su kakamba, wato wani irin kayan lambu ne mai yaɗuwa, da guna, da sāfa, da albasa, da tafarnuwa.

6. Yanzu ranmu ya yi yaushi, ba wani abu, sai dai wannan manna muke gani.”

7. Manna kuwa kamar tsabar riɗi take, kamanninta kuwa kamar na ƙāro ne.

8. Mutane sukan fita su tattara ta, su niƙa, ko kuwa su daka, su dafa, su yi waina da ita. Dandanar wainar tana kamar wadda aka yi da mai.

9. Manna takan zubo tare da raɓa da dad dare a zangon.

Karanta cikakken babi L. Kid 11