Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 10:2-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. “Ka ƙera kakaki biyu na azurfa don ka riƙa kirawo taron jama'a, don kuma ka riƙa sanashe su lokacin tashi daga zangon.

3. Lokacin da aka busa kakaki biyu ɗin gaba ɗaya, sai taron jama'a duka su tattaru a wurinka a ƙofar alfarwa ta sujada.

4. Amma idan ɗaya kaɗai aka busa, sai shugabannin Isra'ila su tattaru a wurinka.

5. Sa'ad da kuka yi busar faɗakarwa, waɗanda suke zaune a gabashin zangon za su tashi.

6. Sa'ad da kuma kuka yi busar faɗakarwa ta biyu, waɗanda suke a kudancin zangon za su tashi. Sai a yi busar faɗakarwa a kowane lokaci da za su tashi.

7. Amma idan za a kira jama'a ne sai a yi busa da ƙarfi amma banda faɗakarwa.

8. 'Ya'yan Haruna, maza, firistoci, su ne za su busa kakakin.“Kakakin za su zama muku ka'ida ta din din din cikin dukan zamananku.

9. Sa'ad da kuka tafi yaƙi a ƙasarku gāba da maƙiyanku da suke matsa muku lamba, sai ku yi busar faɗakarwan nan da kakakin, Ubangiji Allahnku zai tuna da ku, ya cece ku daga maƙiyanku.

10. A ranar murnarku, da lokacin ƙayyadaddun idodinku, da tsayawar watanninku, za ku busa kakakin a lokacin yin hadayunku na ƙonawa, da hadayunku na salama. Za su zama sanadin tunawa da ku a gaban Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.”

11. A rana ta ashirin ga watan biyu a shekara ta biyu, sai aka gusar da girgijen daga kan alfarwa ta sujada.

12. Isra'ilawa kuwa suka tashi daki-daki daga jejin Sinai. Girgijen kuma ya tsaya a jejin Faran.

Karanta cikakken babi L. Kid 10