Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 1:49-54 Littafi Mai Tsarki (HAU)

49. “Sa'ad da kake ƙidaya Isra'ilawa, kada ka haɗa da kabilar Lawi.

50. A maimakon haka, sai ka sa Lawiyawa su zama masu lura da alfarwa ta sujada da kayayyakinta. Za su ɗauki alfarwar da kayayyakinta, su yi aikinta, a zango kuma sai su sauka kewaye da ita.

51. Sa'ad da kuka tashi tafiya, Lawiyawa za su kwankwance alfarwar, su ne kuma za su kafa ta, su ɗaɗɗaure, idan suka sauka a sabon wuri. Idan wani dabam ya zo kusa da alfarwar za a kashe shi.

52. Sauran Isra'ilawa za su sauka ƙungiya ƙungiya, kowane mutum a ƙungiyarsa a ƙarƙashin tutarsa.

53. Amma Lawiyawa za su sauka kewaye da alfarwa ta sujada don su yi tsaronta, domin kada wani dabam ya matsa kusa har ya sa in yi fushi in bugi jama'ar Isra'ila.”

54. Sai Isra'ilawa suka aikata kowane abu da Ubangiji ya umarci Musa.

Karanta cikakken babi L. Kid 1