Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 8:32-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Sauran abin da ya ragu daga naman da abincin, sai ku ƙone su.

33. Ba za ku fita daga cikin alfarwa ta sujada ba har kwana bakwai, wato, sai kwanakin keɓewarku sun cika, gama keɓewarku za ta ɗauki kwana bakwai.

34. Abin da aka yi a wannan rana haka Ubangiji ya umarta a yi domin kafararku.

35. A ƙofar alfarwa ta sujada za ku zauna dare da rana har kwana bakwai, kuna kiyaye umarnin Ubangiji don kada ku mutu, gama haka Ubangiji ya umarta.”

36. Sai Haruna da 'ya'yansa maza suka yi dukan abin da Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.

Karanta cikakken babi L. Fir 8