Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 8:26-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Daga cikin kwandon abinci marar yistin da yake a gaban Ubangiji, ya ɗauki waina guda marar yisti, da waina guda da aka yi da mai, da ƙosai guda. Sai ya ɗibiya su a bisa kitsen da cinyar dama.

27. Ya sa waɗannan abubuwa duka a tafin hannuwan Haruna da na 'ya'yansa maza, ya miƙa abubuwan nan domin hadayar kaɗawa ga Ubangiji.

28. Sa'an nan ya karɓe su daga tafin hannuwansu, ya ƙone su tare da hadaya ta ƙonawa a bisa bagaden don hadayar keɓewa, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

29. Ya kuma ɗauki ƙirjin, ya kaɗa shi don hadayar kaɗawa ga Ubangiji. Wannan shi ne rabon Musa daga cikin ragon keɓewar, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

30. Sa'an nan Musa ya ɗiba daga cikin man keɓewa da jinin da yake bisa bagaden, ya yayyafa wa Haruna da rigunansa, da 'ya'yansa maza da rigunansu. Da haka ya tsarkake Haruna da rigunansa, da 'ya'yansa maza da rigunansu.

31. Sai Musa ya ce wa Haruna da 'ya'yansa maza, “Ku dafa naman a ƙofar alfarwa ta sujada, ku ci shi a wurin, da abincin da yake a cikin kwandon hadayar keɓewa, kamar yadda Ubangiji ya umarta, cewa, Haruna da 'ya'yansa maza za su ci shi.

32. Sauran abin da ya ragu daga naman da abincin, sai ku ƙone su.

33. Ba za ku fita daga cikin alfarwa ta sujada ba har kwana bakwai, wato, sai kwanakin keɓewarku sun cika, gama keɓewarku za ta ɗauki kwana bakwai.

34. Abin da aka yi a wannan rana haka Ubangiji ya umarta a yi domin kafararku.

35. A ƙofar alfarwa ta sujada za ku zauna dare da rana har kwana bakwai, kuna kiyaye umarnin Ubangiji don kada ku mutu, gama haka Ubangiji ya umarta.”

Karanta cikakken babi L. Fir 8