Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 6:2-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Idan wani mutum ya yi laifi na cin amana gāba da Ubangiji, wato, ya yaudari maƙwabcinsa a kan ajiya, ko jingina, ko ƙwace, ko ya zalunce shi,

3. ko ya yi tsintuwa, amma ya yi mūsu har ya rantse da ƙarya, duk dai irin abubuwan da akan aikata na laifi,

4. sa'ad da mutum ya yi laifi, ya kuwa tabbata mai laifi ne, sai ya mayar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta,

5. ko kowane abin da ya rantse a kansa da ƙarya. Zai mayar wa mai abin da abinsa a yadda yake, har ya ƙara da humushin tamanin abin. A ranar da zai yi hadaya don laifinsa, a ranar ce zai mayar wa mai abin da abinsa.

6. Zai kuwa kai wa firist rago marar lahani daga garken tumaki don yin hadaya ga Ubangiji saboda laifinsa. Za a kimanta tamanin ragon daidai da tamanin hadaya don laifi.

7. Firist kuwa zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji, za a kuwa gafarta masa irin laifin da ya yi.

8. Ubangiji kuma ya umarci Musa,

9. ya ba Haruna da 'ya'yansa maza ka'idodin hadayu na ƙonawa. Hadaya ta ƙonawa za ta kwana bisa bagaden, wutar bagaden kuma ta kwana tana ci har safe.

10. Firist zai sa rigarsa ta lilin, ya ɗaura mukurunsa na lilin, sa'an nan ya kwashe tokar hadaya ta ƙonawa daga bagaden, ya zuba a gefensa.

11. Firist ɗin kuma zai tuɓe rigunansa, ya sa waɗansu, sa'an nan ya kwashe tokar ya kai bayan zango ya zuba a wani wuri mai tsabta.

12. Sai a bar wutar bagaden ta yi ta ci, kada a kashe ta. Firist ɗin ya yi ta iza wutar kowace safiya, ya shimfiɗa hadaya ta ƙonawa a jere a bisa wutar, ya kuma ƙone kitsen hadaya ta salama a bisanta.

13. Sai wuta ta yi ta ci a bisa bagaden kullum, kada ta mutu.

14. Wannan ita ce dokar hadaya ta gari. 'Ya'yan Haruna, maza, za su miƙata a gaban Ubangiji daga gaban bagaden.

15. Ɗaya daga cikinsu zai ɗibi lallausan garin hadayar wanda aka zuba masa mai da lubban cike da tafin hannunsa. Zai ƙona wannan a bisa bagaden, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji don tunawa.

16. Haruna da 'ya'yansa maza za su ci ragowar garin. Za a ci shi ba tare da yisti ba a wuri mai tsarki na farfajiyar alfarwa ta sujada.

Karanta cikakken babi L. Fir 6