Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 4:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya kuma ce wa Musa,

2. ya faɗa wa mutanen Isra'ila, in wani ya yi zunubi, ba da gangan ba, har ya karya ɗaya daga cikin dokokin Ubangiji, sai ya bi ka'idodin nan.

3. Idan keɓaɓɓen firist ne ya yi zunubi, ya jawo wa jama'a laifi, sai ya ba da ɗan bijimi marar lahani ga Ubangiji don yin hadaya saboda zunubin da ya aikata.

4. Zai kawo ɗan bijimin a ƙofar alfarwa ta sujada a gaban Ubangiji, ya ɗibiya hannunsa a kan kan bijimin, ya yanka shi a gaban Ubangiji.

5. Shi kuma keɓaɓɓen firist ɗin ya ɗibi jinin bijimin ya kai shi a alfarwa ta sujada.

6. Ya tsoma yatsansa cikin jinin, ya yayyafa jinin sau bakwai a gaban Ubangiji a wajen labulen Wuri Mai Tsarki.

7. Zai kuma ɗiba daga cikin jinin, ya sa a bisa zankayen bagaden ƙona turaren da suke cikin alfarwar a gaban Ubangiji. Sauran jinin bijimin kuwa zai zuba shi a gindin bagaden ƙona hadaya wanda yake a ƙofar alfarwa ta sujada.

8. Zai ɗebe dukan kitsen ɗan bijimi na yin hadaya don zunubi, da kitsen da yake rufe da kayan cikin, da wanda yake bisansa,

9. da ƙodoji biyu da kitsen da yake bisansu wajen kwiɓi, da matsarmama.

Karanta cikakken babi L. Fir 4