Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 26:11-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Zan kafa wurin zamana a tsakiyarku, ba kuwa zan gaji da ku ba.

12. Zan yi tafiya tare daku, in zama Allahnku, ku kuma ku zama mutanena.

13. Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, don kada ku zama bayinsu. Na karya ikonsu da yake danne ku, na bar ku ku yi tafiya a sake.”

14. “Amma idan ba za ku kasa kunne gare ni ba, to, za ku sha hukunci.

15. Idan kuma kuka yi watsi da dokokina, ba ku kuwa kula da ka'idodina ba, har kuka ƙi kiyaye umarnaina, kuka karya alkawarina,

16. to, zan hukunta ku. Zan aukar muku da bala'i, da cuce-cuce da ba su warkuwa, da zazzaɓin da zai lalatar muku da ido, rai zai zama muku da wahala. Za ku yi shuka a banza gama maƙiyanku ne za su ci.

17. Zan yi gāba da ku in sa maƙiyanku su ɗibge ku, waɗanda suke ƙinku za su mallake ku. Za ku yi ta gudu ba mai korarku.

18. “Amma idan duk da haka ba ku kasa kunne gare ni ba, sai in tsananta hukuncinku har sau bakwai saboda zunubanku.

19. Zan karya ikonku wanda kuke fariya da shi, in hana ruwan sama, ƙasa kuma ta zama kamar tagulla.

20. Za ku ɓarnatar da ƙarfinku a banza gama ƙasarku ba za ta ba da amfaninta ba, itatuwan ƙasar kuma ba za su ba da 'ya'ya ba.

21. “Idan har yanzu kuka tayar mini, ba ku kasa kunne gare ni ba, sai in ƙara yawan hukuncinku har sau bakwai, saboda zunubanku.

22. Zan kuwa turo muku mugayen namomin jeji waɗanda za su kashe 'ya'yanku, su hallakar da dabbobinku, su sa ku zama kaɗan, har ba mai gilmayya a hanyoyinku.

23. “Idan wannan hukunci bai sa kun juyo gare ni ba, amma kuka ci gaba da tayar mini,

24. sai in hau ku da hukunci, har ya fi na dā riɓi bakwai saboda zunubanku.

25. Zan sa a kawo muku yaƙi saboda karya alkawarina da kuka yi. Idan kuwa kun tattaru a cikin biranenku, sai in aukar muku da masifa, in bashe ku ga maƙiyanku.

26. Zan katse abincinku, mata goma za su dafa abincinku a murhu ɗaya, su rarraba muku shi da ma'auni. Za ku ci, amma ba za ku ƙoshi ba.

Karanta cikakken babi L. Fir 26