Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 25:9-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. A ranar kafara, goma ga wata na bakwai za su busa ƙahon rago da ƙarfi cikin ƙasarsu duka.

10. Shekara ta hamsin kuwa za su keɓe ta, su yi shelar 'yanci cikin ƙasar duka ga dukan mazaunanta. Za ta zama shekarar murna a gare su. Kowa zai koma mahallinsa, ko wannensu kuma wurin danginsa.

11. Shekarar nan ta hamsin za ta zama shekara ta murna a gare su. A cikinta ba za su yi shuka, ko su girbe gyauro ba, ba kuwa za su tattara 'ya'yan inabin da ba su yi wa aski ba.

12. Shekara ce ta murna, za ta zama keɓaɓɓiya a gare su. Za su ci albarkar da gonakin suka bayar.

13. Ubangiji ya ce, “A wannan shekara ta hamsin ta murna kowa zai koma mahallinsa.

14. In ka sayar, ko ka sayi gona a wurin ɗan'uwanka, Ba'isra'ile, kada ku cuci juna.

15. Idan za ka yi sayayya a wurin maƙwabcinka, sai ka lura da yawan shekarun da za ka mora kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo.

16. Idan shekarun sun ragu da yawa kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo, sai ka saya da tsada. Idan kuwa shekarun sun ragu kima ne, sai ka saya da araha, gama yana sayar maka bisa ga yawan shekarun da za ka mora ne.

17. Kada ku cuci juna fa, amma ku ji tsoron Allahnku, gama ni ne Ubangiji Allahnku.”

18. “Domin haka sai ku kiyaye farillaina, da ka'idodina. Ku aikata su domin ku zauna a ƙasar lami lafiya.

19. Ƙasar za ta ba da amfani, za ku ci, ku ƙoshi, ku zauna lafiya.

20. “Idan kuwa kun tambaya abin da za ku ci a shekara ta bakwai, idan ba za ku yi shuka ba, ba kuwa za ku tattara amfanin gona ba,

21. ku sani zan sa muku albarka a shekara ta shida don ta ba da isasshen amfanin da zai kai ku shekara uku.

22. Sa'ad da za ku yi shuka a shekara ta takwas, shi ne za ku yi ta ci, har shekara ta tara lokacin da za ku yi girbi.”

23. “Kada a sayar da gona din din din, gama ƙasar tawa ce, ku kuwa baƙi na da kuke baƙunci a wurina.

24. “Amma kuna iya jinginar da gonar da kuka mallaka.

25. Idan ɗan'uwanka ya talauce, har ya jinginar maka da mahallinsa, sai danginsa na kusa ya fanshi abin da ɗan'uwansa ya jinginar.

26. Idan mutumin ba shi da wanda zai fansa, idan shi kansa ya arzuta, ya sami abin da ya isa yin fansa,

27. to, sai ya lasafta yawan shekarun da ya jinginar da abin, sa'an nan ya biya jinginar daidai da shekarun da suka haura kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo, shi ya koma kan mahallinsa.

Karanta cikakken babi L. Fir 25