Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 25:18-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. “Domin haka sai ku kiyaye farillaina, da ka'idodina. Ku aikata su domin ku zauna a ƙasar lami lafiya.

19. Ƙasar za ta ba da amfani, za ku ci, ku ƙoshi, ku zauna lafiya.

20. “Idan kuwa kun tambaya abin da za ku ci a shekara ta bakwai, idan ba za ku yi shuka ba, ba kuwa za ku tattara amfanin gona ba,

21. ku sani zan sa muku albarka a shekara ta shida don ta ba da isasshen amfanin da zai kai ku shekara uku.

22. Sa'ad da za ku yi shuka a shekara ta takwas, shi ne za ku yi ta ci, har shekara ta tara lokacin da za ku yi girbi.”

23. “Kada a sayar da gona din din din, gama ƙasar tawa ce, ku kuwa baƙi na da kuke baƙunci a wurina.

24. “Amma kuna iya jinginar da gonar da kuka mallaka.

25. Idan ɗan'uwanka ya talauce, har ya jinginar maka da mahallinsa, sai danginsa na kusa ya fanshi abin da ɗan'uwansa ya jinginar.

26. Idan mutumin ba shi da wanda zai fansa, idan shi kansa ya arzuta, ya sami abin da ya isa yin fansa,

27. to, sai ya lasafta yawan shekarun da ya jinginar da abin, sa'an nan ya biya jinginar daidai da shekarun da suka haura kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo, shi ya koma kan mahallinsa.

28. Amma idan ba shi da isasshen abin da zai fanshi abinsa, to, sai wanda ya karɓi jinginar ya ci gaba da riƙon abin da aka jinginar masa ɗin har shekara ta hamsin ta murna, a lokacin ne zai mayar wa mai shi, mai shi ɗin kuwa ya koma a kan mahallinsa.

Karanta cikakken babi L. Fir 25