Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 24:10-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ɗan wata mace Ba'isra'iliya wanda mahaifinsa Bamasare ne, ya fita, ya yi faɗa da wani Ba'isra'ile a cikin zangon.

11. Sai ɗan Ba'isra'iliyar ya saɓi sunan Allah. Aka kai shi wurin Musa. Sunan mahaifiyar kuwa Shelomit 'yar Dibri na kabilar Dan.

12. Musa kuwa ya kulle shi a gidan tsaro kafin Ubangiji ya faɗa musu abin da za su yi da shi.

13. Sai Ubangiji ya ce wa Musa,

14. “Fito da wanda ya yi saɓon nan daga cikin zangon. Ka kuma sa dukan waɗanda suka ji shi su sa hannuwansu a bisa kansa. Taron jama'ar kuwa su jajjefe shi da duwatsu.

15. Sa'an nan ka faɗa wa Isra'ilawa, cewa, duk wanda ya saɓi Allah zai ɗauki alhakin zunubinsa,

16. za a kuwa kashe shi. Duk Ba'isra'ile ko baƙon da yake zaune cikin Isra'ilawa wanda ya saɓi Allah, sai taron jama'a su jajjefe shi da duwatsu ya mutu.

17. “Duk wanda ya kashe mutum, shi ma sai a kashe shi.

18. Wanda ya kashe dabba kuma ya yi ramuwa, rai maimakon rai.

19. “Idan mutum ya yi wa wani rauni, kowane irin rauni ne ya yi masa, shi kuma haka za a yi masa.

20. Idan ya karya masa ƙashi ne, sai a karya nasa ƙashin, idan ya cire wa wani ido, sai a ƙwaƙule nasa, idan haƙori ya ɓalle, sai a ɓalle nasa. Duk irin raunin da ya ji wa wani haka za a yi masa.

21. Wanda ya kashe dabba ya yi ramuwa, wanda kuwa ya kashe mutum sai a kashe shi.

22. Irin shari'ar da za a yi wa baƙo, ita za a yi wa ɗan gari, gama ni ne Ubangiji Allahnku.”

23. Sai Musa ya yi magana da Isra'ilawa, suka kuwa fito masa da mutumin da ya yi saɓon a bayan zangon. Suka jajjefe shi da duwatsu. Haka Isra'ilawa suka aikata yadda Ubangiji ya umarci Musa.

Karanta cikakken babi L. Fir 24