Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 2:4-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sa'ad da aka kawo hadaya ta gari da aka toya cikin tanda, sai a yi shi da gari mai laushi marar yisti kwaɓaɓɓe da mai, a shafa masa mai, a toya, ko kuwa a soya ƙosai.

5. Idan kuwa hadayar ta gari ce da aka toya cikin kaskon tuya, sai a yi abinci da gari mai laushi wanda ba a sa masa yisti ba, wanda aka kwaɓa da mai.

6. Za a gutsuttsura shi, a zuba masa mai, hadayar gari ke nan.

7. Idan kuma hadayar ta gari ce wadda aka dafa cikin tukunya, ita kuma, sai a yi ta da gari mai laushi da mai.

8. Za a kawo hadaya ta gari da aka yi da abubuwan nan ga Ubangiji. Sa'ad da aka kai wa firist, sai ya kawo ta a bagaden.

Karanta cikakken babi L. Fir 2